Dandalin Yanar Gizo na Gwamnatin Amurka a hukumance

Game da mu

Mahangar Shirin

Tarihin Shirin da Hukumomin kula da tanadin da aka yi a bisa doka

An ƙaddamar da RFJ, wanda ke shiri ne na ba da lada na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, a ƙarƙashin Dokar Yaƙi da Ta’addanci ta 1984, da Dokar Jama’a 98-533 (wadda aka yi wa laƙabi da 22 U.S.C § 2708). Shirin da Sashen Tsaro na Difilomasiyya a Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ke gudanarwa, manufar RFJ ita ce ba da lada don samun bayanan da za su kare rayukan Amurkawa da kadarorin Amurka da kuma inganta tsaron ƙasa.

Tun daga shekarar 1984, Majalisa ta faɗaɗa shirin RFJ don ya ƙunshi ba da lada a kan manyan abubuwa uku:

 • Ta’addanaci. Bayanan da suka:
  • Kai ga kamawa ko gurfanarwa a gaban kotu na mutumin da ya shirya, ko ya aikata, ko ya yi yunƙurin aikata ta’addanci tsakanin ƙasa da ƙasa a kan Amurkawa ko dukiyoyi a Amurka ko a ƙasar waje;
  • Daƙile faruwar waɗannan ayyuka kwata-kwata;
  • Tantancewa ko gano inda wani jagoran ta’addanci yake;ko
  • Katse ayyukan samun kuɗi na wasu ƙungiyoyin ta’addanci. Wannan ya haɗa da daƙile ƙungiyoyin garkuwa da mutane da kuma ayyukan garkuwar da ke taimaka musu wajen samun kuɗi.
 • Kutse a Harkokin Zaɓe. Bayanan da suka:
  • Kai ga ganowa ko zuwa inda wani mutum yake a ƙasar waje da ke aikata kutse a harkoin zaɓe da gangan, ciki har da ayyukan da suka saɓa wa dokar ‘yancin zaɓe, ko kuma duk wani aiki da wani yake yi a matsayin wakili ko madadin wata gwamnatin wata ƙasar waje ko kuma ƙungiya.
  • Kai ga daƙilewa ko lalatawa ko kuma yadda za a warware wani aikin kutse a harkokin zaɓe.
 • Ayyukan Mugunta a Intanet. Bayanan da suka:
  • Tantance ko gano wani mutum wanda yayin da yake aiki bisa umurnin ko ƙarƙashin gwamnatin wata ƙasar waje, yake taimakawa tare da ƙarfafa gwiwa wajen karya Dokar Zamba ta Intanet (“CFAA”), 18 U.S.C.§ 1030. Wannan ya ƙunshi yin katsalandan a harkokin zaɓe daga ƙasar waje.
 • Koriya ta Arewa. Bayanan da suka:
  • Katse harkokin samun kuɗi na wasu mutane ko cibiyoyi da ke taimaka wa gwamnatin Koriya ta Arewa ta hanyar wasu ayyuka;ko
  • Tantance ko gano inda wani mutum da ke aiki bisa jagoranci ko umurnin gwamnatin Koriya ta Arewa yake, ko ya taimaka tare da ƙarfafa gwiwa wajen karya Dokar Zamba ta Intanet (“CFAA”), 18 U.S.C.§ 1030. Wannan ya ƙunshi kai hare-haren ta intanet da kutse a tsare-tsaren gwamnatin Amurka.

Tallata Tayin Lada

Da zarar Sakataren Harkokin Waje ya amince da tayin lada, RFJ zai tallata shi ga waɗanda ya dace bisa al’adunsu mafiya dacewa ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa daban-daban, ciki har da shafukan sada zumunta, da na tura saƙonni, da kuma kafofin yaɗa labarai da aka saba.

Tafiyar da Ba Da Bayanai

RFJ na umartar mutane su tura saƙon bayanai ga layukansa na musamman a harsuna na musamman ta hanyar amfani da manhajojin tura saƙo masu tsaro, waɗanda suka haɗa da Signal, da Telegram, da WhatsApp. Mutane ka iya tura bayanai ta saƙon imel da kuma shafukan zumunta. RFJ na tura bayanan da suka dace ga sauran hukumomin gwamnatin Amurka.

Biyan Lada

Idan bayanan da mai ba da bayanai ya ba da bayanan da suka samar da sakamako mai kyau, hukumar da ke aiki a kan lamarin za ta iya miƙa sunansa don a biya shi lada. Kwamatin hukumomi ne ke tantance sunan wanda za a miƙa sunansa sannan ya miƙa shi ga Sakatare don ya yanke shawarar a biya ko kar a biya.

Tun bayan ƙaddamar da shi a 1984, shirin ya biya ladan da ya kai fiye da dala miliyan 250 ga mutum sama da 125 a faɗin duniya da suka ba da bayanai masu amfani, waɗanda suka taimaka wajen inganta tsaron Amurka.

SUBMIT A TIP

Do Your Part. Secure a Safer World.

There are many ways to submit information to Rewards for Justice.

You may choose from multiple platforms and contact us in numerous languages. To process your information efficiently, we ask you to state your information as succinctly as possible, provide your name, location, and preferred language, and upload all relevant files such as photographs, videos, and documents to support your information. An RFJ representative will soon contact you. Please be patient, as RFJ reads every tip we receive.

Please visit our Tor-based tips-reporting channel at: he5dybnt7sr6cm32xt77pazmtm65flqy6irivtflruqfc5ep7eiodiad.onion

Turo da Bayani

Ba da gudummawarku Samar da Duniya Mai Kwanciyar Hankali.

Akwai hanyoyi da yawa da za ku iya turo da bayani.

Za ku iya zaɓa daga wurare daban-daban kuma tuntuɓe mu a harsuna daban-daban. Don yin aiki da bayananku yadda ya kamata, muna buƙatarku da ku zayyana bayananku ƙarara, ku saka sunanku, da wurin da kuke, da harshen da kuka fi so, sannan ku ɗora dukkan takardun da suka dace, kamar ƙaramin hoto, da bidiyo da za su ƙarfafi bayanan naku. Jami’in shirin RFJ zai tuntuɓe ku nan gaba kaɗan. Muna roƙo da ku ƙara haƙuri saboda muna karanta dukkan bayanan da muka samu.

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Signal don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Telegram don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Ku duba shafin da zai ba ku ƙarin bayani game da turo rahoto a: he5dybnt7sr6cm32xt77pazmtm65flqy6irivtflruqfc5ep7eiodiad.onion

Skip to content